Ana ci gaba da zaben ′yan majalisar dokoki a Turkiya | Labarai | DW | 01.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da zaben 'yan majalisar dokoki a Turkiya

Zaben majalisar dokokin kasar ta Turkiya zai tantance inda gwamnatin za ta fuskanta.

Ana ci gaba da kada kuri'a a zabe kasa baki daya da ke wakana a kasar Turkiya, inda jam'iyya mai mulki ta AKP take fata kan samun kujerun majalisar dokoki da take bukata domin samun damar kafa gwamnati kai tsaye.

A zaben watan Yuni, kimanin watanni biyar da suka gabata, jam'iyyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan mai mulki ta rasa rinjayen da take bukata a karo na farko cikin shekaru 13, abin da ya haifar da rashin iya kafa gwamnati, da ya janyo sake kiran zabe karo na biyu a shekara guda, a kasar mai mutane kimanin milyan 80. An jibge dubban jami'an tsaron musamman cikin yankunan Kurdawa na kasar ta Turkiya, saboda tabbatar da doka da oda.