1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da tashe tashen hankula a fadin kasar Iraki

September 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buku

Akalla mutane 46 aka halaka sannan wasu da dama suka jikta a jerin hare haren bama-bamai da rokoki da aka kai a Bagadaza babban birnin Iraqi. Da farko ofishin jakadancin Birtaniya ya ce wani ayarin motocin jami´ansa ya tsallake rijiya da baya a fashewar wani bam da aka dana a gefen hanya a kusa da unguwar nan ta jami´an diplomasiya mai cike da tsauraran tsaro. ´Yan sanda a Bagadaza sun ce mutane 9 sun rasu a lardin Diyala dake arewa da babban birnin na Iraqi. Sannan rundunar sojin Amirka ta ce an halaka sojin ta daya a wani harin bam da aka kai a lardin Anbar. Ma´aikatar kiwon lafiya ta Iraqi ta ce a cikin watan agusta ta yi rajistar mutane 973 daukacin su fararen hula da aka hallaka su a tashe tashen hankula. Wannan adadi bai kai yawan mutane dubu 3 da 500 da aka kashe a cikin watabn yuli ba.