1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba barin wuta a Libiya

April 21, 2019

Sabbin hare-hare daga bangarori masu gaba da juna a Tripoli babban birnin kasar Libiya na daukar hankalin kasashen duniya, daidai lokacin da ayuka ke salwanta.

https://p.dw.com/p/3HBMj
Libyen | Libyens international anerkannte Regierungstruppen schießen bei Kämpfen mit östlichen Truppen in Ain Zara
Hoto: Reuters/H. Amara

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya, na tsanata kai farmaki kan mayakan madugun yaki Khalifa Haftar, daidai lokacin da bangaren na Haftar ke tinkarar mashigar Tarabulus babban birnin kasar.

An kwashe daren da ya gabata ana ta jin rugugin manyan makamai, a luguden wuta da ke wakana tsakanin bangarorin kasar da ke yaki da juna.

Hare-hare ta sama da harbe-harben makamai masu linzami gami da tashin nakiyoyi su ne suka mamaye yankunan da bangarorin suka ja daga a yankin na Tarabulus

Hukumomi sun sake bude filin jirage daya tilo da ya saura a birnin, wanda aka garkame shi da fari dama hanyoyin sararin samaniya.