An yi wa Tsvangirai ban kwana | Labarai | DW | 19.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa Tsvangirai ban kwana

Dubban al'umar Zimbabuwe ne suka mamaye titunan Harare a wannan Litinin don girmama marigayi madugun adawar kasar Morgan Tsvangirai.

Wahlkampfveranstalatung der MDC in Simbabwe (AFP/Getty Images/Z. Auntony)

Wasu daga cikin masu juyayin rashin Tsvangirai

Dudun dubatan al'umar kasar Zimbabuwe ne suka bazu a titunan Harare a wannan Litinin don girmama marigayi madugun adawar kasar Morgan Tsvangirai. Magoya bayan marigayi Tsvangirai wanda tsohon Firaminista ne a kasar, sun fito ne sanye da tufafi masu launin jam'iyyarsa ta MDC.

Akwai ma wasu 'yan kasar daga ketare da suka kasance cikin jerin masu alhinin rashin marigayin, da ake ganin jigo ne da ba za a taba mantuwa da shi a tarihin demokradiyyar kasar ba. A jiya Lahadi ne kuma shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar ya ziyarci mahaifar marigayi Tsvangirai. Shi ma madugun adawa a kasar Kenya wanda ya nada kansa matsayin shugaban al'uma Raila Odinga ya kasance a lokacin wannan juyayi.