An yi mummunar ambaliyar ruwa a kasar Japan | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi mummunar ambaliyar ruwa a kasar Japan

Ambaliyar ruwa a wasu biranen gabashin Japan ta yi barna mai yawa, inda ta yi awan gaba da gidaje da motoci sannan madtsun ruwa sun rushe.

Ruwan sama mai yawa ya janyo mummunar ambaliyar ruwa da zaizayewar kasa a gabashin kasar Japan. Rahotanni sun ce ruwan ya yi barna mai yawa a birnin Joso mai yawan mazauna dubu 65 da ke arewa da Tokyo babban birnin kasar ta Japan. Kogin Kinugava da ke yankin ya batse kana laka mai yawa ta malala cikin garin inda ta yi awan gaba da gidaje da motoci. Cikin dimuwa mazauna sun hau kan rufin gidajensu suna jiran a kai musu dauki. A garin Minami Aizu ruwan ya karya wata gada sannan ya tafi da daruruwan gidaje kamar yadda mahukunta suka nunar. A garin Kanuma haka lamarin yake inda madatsun ruwa suka rushe sakamakon ambaliyar. Sannan a tashar nukiliya ta Fukushima ruwan da ya gurbata da sinadaran atom ya malala cikin kogi.