1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jana'izar 'yar jaridar Aljazeera

Ramatu Garba Baba
May 13, 2022

Dubban dubata ne suka halarci jana'izar 'yar jaridar Aljazeera Shireen Abu Akleh da aka kashe a bakin aiki a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Larabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4BEpz
Trauer um Shireen Abu Akleh
Hoto: Muammar Awad/Xinhua/IMAGO

A wannan Juma'a aka gudanar da jana'izar 'yar jaridar ta shahararriyar kafar yada labaran Al Jazeera Shireen Abu Akleh, an binne Akleh a wata makabarta kusa da kushewar iyayenta a birnin Jerusalem kwanaki biyu bayan mutuwarta. Kawo yanzu, ba a kai ga tantance bangaren da ke da hannu a kisan 'yar jaridar ba a tsakanin Isra'ila da Falasdinu da ke zargin juna da alhakin kisan.

Shireen na kan aikin tattara rahoto a lokacin da ta gamu da ajalinta a Gabar Yamma da Kogin Jordan, ta kwashe fiye da shekaru 25 tana aikin aika wa tashar ta Aljazeera rahotann. Shireen dai, ta rasu tana da shekaru 51 a duniya. 

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun yi kira na a gudanar da bincike mai zaman kanshi kan kisan gillar da aka yi wa Shireen. Tuni wata gamayyar kungiyoyin 'yan jaridun Larabawa da kasashen Yamma suka sanar da kafa wata kungiyar mai suna "Sheereen" sunan yar jaridar domin ganin an bi  hakkin 'yan jaridun da ake kashewa a fadin duniya domin tallafawa iyalansu.