1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi gangami kan muhalli a Jamus

Ahmed Salisu
June 21, 2019

Dubban yara 'yan makaranta ne a wannan Juma'ar suka hadu a birnin Aachen da ke yammacin Jamus don yin gangami da nufin jan hankalin hukumomi kan su kara azama wajen daukar matakai na kare muhalli.

https://p.dw.com/p/3KrqK
Deutschland | Klimademonstration Fridays for Future - Aachen
Hoto: imago images/J. Tack

Gangamin da ake yi wa lakabi da Fridays for Future wanda shi ne irinsa na farko da aka yi a birnin ya hada kan dalibai akalla dubu arba'in kuma wanda suka shaida faruwarsa sun ce shi ne mafi girma da aka taba gani a kasar.

Daliban dai sun yi gangamin ne a gaban filin wasan nan na Tivoli a Aachen din wanda ke kusa da wajen da ake hakar Ma'adanin Kwal a kasar wanda shi ne waje mafi girma a nahiyar Turai da ake fidda sinadarin Carbon Dioxide da ke gurbata muhalli.

Mai magana da yawun wanda suka shirya gangamin Fridays for Future na yau Cornelia Theuer ta ce an samu wakilcin dalibai daga kasashe bakwai wanda suka hada da Holland da Beljiyam da Faransa da Burtaniya.