An tsintsi gawarwaki ′ya cirani a Evros | Labarai | DW | 10.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsintsi gawarwaki 'ya cirani a Evros

Hukumomin kiwon lafiya a Girka sun ce an tsintsi gawarwakin 'yan cirani guda shida a kan iyaka tsakanin Turkiya da Girkar a Evros wanda tsananin sanhin hunturu da ake yi, ya kashesu.

'Yan cirani wadanda suka hada da mata biyu 'yan kasashen Afirka da samari 'yan kimanin shekaru 18 zuwa 30 sun mutu sakamakon yadda jininsu ya yi kasa saboda kadawar sanhi. Babu dai wani karin bayyani da aka samu dangane da 'yan cirani a game da kasashen da suka fito. Yankin Evros da ke tsakanin Girka da Turkiya wanda aka raba kan iyakar da katagan mai tsawon mita 12 nanade da waya, duk da haka ya zama  wata hanyar da 'yan cirani suke kurdawa domin shiga Turai daga Turkiya zuwa Girka.