An tsawaita wa′adin taron sauyin yanayi na Paris | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsawaita wa'adin taron sauyin yanayi na Paris

Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya bayyana dage rufe taron sauyin yanayin zuwa gobe Asabar bayan da har kawo yanzu aka gaza samun matsaya tsakanin mahalarta taron kan yarjejeniyar karshe.

Ministan harakokin wajen Faransa kana jagoran taron sauyin yanayi na duniya da ke gudana a birnin Paris na kasar ta Faransa ya bayyana tsawaita wa'adin zaman taron da kwana daya bayan da taron ministoci da ke nazarin kundin jerin shawarwarin da kasashen duniya suka bayar ya gaza samun matsaya kawo yanzu.

Batun rage dumamar yanayin da digri biyu ko daya da rabi a ma'aunin zafi na Celcius dama na kudaden daukar dawainiyar ayyukan rage kaifin illar da dumamar yanayin ke yi a kasashe masu tasowa tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da masu tasowa na kasancewa batutuwan da ke ci gaba da kawo tsaiko wajen cimma yarjejeniyar ta karshe.

Ministan laurent Fabius ya ce yana sa ran gabatar da yarjejeniyar wucan gadi ga zauran taro a safiyar gobe Assabar.