An tsaurara matakan tsaro a Rasha | Labarai | DW | 29.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsaurara matakan tsaro a Rasha

Wani harin ƙunar baƙin wake ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18 a Rasha

Wata 'yar ƙunar baƙin wake ɗauke da bam ta hallaka mutane 18, yayin hari a wata tashar jirgin ƙasa cikin yankin kudancin ƙasar Rasha. Akwai wasu mutanen kimanin 50 da suka samu raunika.

Wannan hari na garin Volgograd ya janyo Shugaban Vladimir Putin neman ganin jami'an tsaro sun kara ƙaimi, musamman yayin da ƙasar ke shirin ɗaukar nauyin gasar guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, Olympics na lokacin hunturu, wanda ake farawa a farkon watan Febrairu na shekara mai kamawa ta 2014.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane