An tsagaita wuta tsakanin Isra′ila da Hamas | Labarai | DW | 26.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas

Hare-hare tsakanin Isra'ila da Falasdinu na kara zafi cikin 'yan kwanakin nan, daidai kuma lokacin da ake makonni biyu da zaben kasa a Isra'ilar.

Isra'ila ta kai hare-hare kan wasu yankunan falasdinawa da ke a zirin Gaza, hare-haren da ke matsayin martani kan wani harin rokoki da falasdinawan suka kaddamar kan Tel Aviv a jiya Litinin.

Kungiyar Hamas ta falasdinawan ta ce tuni aka cimma yarjejeniyar tsagaita buda wa juna wuta. A cewar Hamas, kasar Masar ce ta shiga tsakani, wanda ya kai ga cimma nasarar yarjejeniyar.

Martanin Isra'ilar dai na zuwa ne yayin da Firaminista Netanyahu ya nuni fushi kan harin da ya shafi birnin Tel Aviv da ya jikkata mutane bakwai. Babu dai wasu rahotannin da suka nuna irin ta'asarar da aka tafka a Gaza a sabon harin kawo i yanzu.