1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An toshe shafin Facebook a Myanmar

February 4, 2021

Hukumomin da ke jagorantar al'amura a Myanmar, sun dauki matakin hana yaduwar bayanai ta kafofin sada zumunta a kokarin hana tashin tarzoma.

https://p.dw.com/p/3oqt4
Bangladesch Geflüchtete Rohingya Myanmar Putsch Aung San Suu Kyi
Hoto: Abdur Rahman/DW

Sabuwar gwamnatin mulkin soja a Myanmar, ta toshe hanyoyin sadarwar kafar sada zumunta ta Facebook a kasar, sakamakon yadda wasu ke amfani da kafar wajen kiraye-kirayen zanga-zanga.

Hakan ya biyo bayan kifar da gwamnatin tsohuwar jagorar kasar, Aung San Suu Kyi, a ranar Litinin da ta gabata.

Kafar sadarwar ta Facebook dai na da matukar farin jini a kasar ta Myanmar, inda kuwa jami'an tsohuwar gwamnatin da sojojin kasar suka kifar ke amfani da ita wajen gabatar da bayanai da ma wasu manufofi.

Da yammacin ranar Laraba ne masu amfani da Intanet din suka soma sanar da labarin toshe Facebook din.

Kamfanonin sadarwa a kasar sun fitar da sanarwar da ke tabbatar da rufe Facebook din na wucin gadi, bayan samun umurnin yin hakan daga gwamnatin sojin kasar.