1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tattaunawa kan makomar Mali

Mahamadou Kane Rakia Arimi/SB
April 16, 2024

A Mali an fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin rikon kwarya da al'umma a duk yankunan kasar misali a birnin Bamako ana gudanar da tattaunawar domin tsayar da shawara da za su gabatar wa mahukunta.

https://p.dw.com/p/4erD6
Mali I Assimi Goita shugaban gwamnatin rikon kwarya
Assimi Goita shugaban gwamnatin rikon kwaryar MaliHoto: Fatoma Coulibaly/REUTERS

Jamaa da dama ne suka halarci zaman shawarwarin, wadanda suka yi kwaskwarima ta karshe ga irin shawarwarin da aka cimma. Batutuwan da aka fi mayar da hankali su ne batun samar da zaman lafiya da sake sasanta tsakanin al'ummar kasar da kuma batutuwa na tattalin arziki da na siyasa. Mohamed Traoré, wanda aka fi sani da Bill, memba ne na kungiyar Résistance citoyenne wanda ya nuna bukatar ganin 'yan siyasa sun shiga tattaunawar inda ya ce babu shakka mutane sun amsa kira a wannan gayyata, kama daga wakilan kungiyoyin farar hula da magabata na gargajiya da masana, duk sun kasance a cikin wannan tattaunawa.

Karin Bayani: Sojojin Mali sun haramta al'amuran siyasa a fadin kasar

 

Mali I Magoya bayan sojojin Mali da ke mulki
Magoya bayan sojojin Mali da ke mulkiHoto: Fatoma Coulibaly/REUTERS

A karshen tattaunawar, mahalarta taron sun ba da shawarar kafa aikin 'yan sanda a cikin gunduma ta II inda kuma suka yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin jama'a da jami'an tsaro. Cissé Kadidia Haidara, 'yar takara, na mai da hankali kan hadin kai da zamantakewa. Ta kuma ba da shawarar rage salon tsadar rayuwar kasar da gudummawar 'yan kasa, gami da yaki da ta'addanci.

Tattaunawar tsakanin 'yan Mali, tattaunawa ce da ke da nufin gano tushen tashe-tashen hankula a kasar, da yin rigakafi da kuma kawo karshe tashe-tashen hankulan, ta hanyar inganta hanyoyin tafiyar da duk wasu abubuwan da suka taso daga kasar ta Mali, don shawo kan rikice-rikice da kuma tabbatar da zaman lafiya.