1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rusa kungiyar dalibai ta jawo damuwa a kasar Mali

Nafissa Amadou Mohamed Tidjani Hassane/Mouhamadou Awal Balarabe
March 21, 2024

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun suffanta rusa kungiyar daliban Mali da tauye 'yancin walwala a kasar ta Yammacin Afrika. Gwamnatin Assimi Goita ta soja na zargin ta da wasu kungiyoyin siyasa da haddasa rikice-rikice.

https://p.dw.com/p/4dyAh
Daliban Mali na fuskantar kalubale tun bayan juyin mulkin soja
Daliban Mali na fuskantar kalubale tun bayan juyin mulkin soja Hoto: Michele Cattani/AFP

Matakin rusa uwar kungiyar daliban Mali ya biyo bayan mutuwar wani dalibi na Jami'ar Bamako da jikkatar wasu dalibai da dama a makonin da suka gabata sakamakon arangama tsakanin bangarorin da ke hamaya kan halastcin jagororin kungiyar da ake wa lakabi da AEEM. Hasali ma, rikicin ya sa an tasa keyar shugaban kungiyar da wasu takwarorinsa takwas i zuwa gidan yari, tare da tayar da tsohon miki na zargin kungiyar da zama ummul aba'isin duk rikice-rikice da ke aukuwa a makarantun Mali.

Rashin cika alkawari kan tsaron makarantu

Kungiyar dalibai ta AEEM ta saba gudanar da zanga-zanga kan baututuwan siyasa
Kungiyar dalibai ta AEEM ta saba gudanar da zanga-zanga kan baututuwan siyasaHoto: Habibou Kouyate/AFP

Sai dai matakin rusa kungiyar AEEM ya zo wa dalibai a ba-zata in ji wani dalibi da ya bukaci a sakaye sunansa bisa dalilai na tsaro, inda ya ce: : Wannan laifi, gwamnati ce ya kamata ta dauki alhakinsa. A shekararar 2016 a yayin babban taron da aka gudanar kan rashin tsaro a makarantu da jami'o'i, an fitar da jaddawalin hanyoyin da hukumomi za su bi don magance wannan matsala. Sai dai ba a aiwatar da ko guda daga cikin wadannan shawarwaru ba''

Karin bayani:Abzinawan Mali sun yi fatali da tayin tattaunawa

Abin da ke daukar hankalin a ciki da wajen Mali shi ne yadda aka samu makamai da makudan kudade a lokacin da jami'an tsaro suka kai sumame a ofishin kungiyar daliban, lamarin da ake dasa ayar tambaya kan ko wannan ne ya kai gwamnatin mulkin soja daukar wannan mataki soke kungiyar. Amma a mahangar wani tsohon jagoran dalibai, rusa kungiyar ta AEEM ba shi ne mafita ba. Ya ce: " Muhimmin abu a nan shi ne sauya fasalin dokokin kungiyar da kuma yin gyara-gyare ga ka'idojin zaben shugabannita domin  ta taka rawa wajen kafuwar dimukuradiyya a Mali."

Neman murkushe masu adawa da mulkin sojia

Kungiyar da Malamin addini Imam Dicko ya kafa ba ta tsira daga rasawa ba
Kungiyar da Malamin addini Imam Dicko ya kafa ba ta tsira daga rasawa baHoto: AFP/A. Riesemberg

Rusa uwar kungiyar daliban Mali na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Assimi Goita da ke neman dawwama kan madafun iko ta fara yi wa kungiyoyin fararen hula bita da kulli. Wanda ya fi daukar hankali shi ne rusa gamayyar kungiyoyin da ke goyon bayan shehin Malami Imam Mahmoud Dicko wanda ya dawo daga rakiyar sojoji. A cewar lauya mai zaman kansa kuma dan gwagwarmaya Maitre Mahamadou Ismael Konate, wannan na fito da aniyar gwamnatin sojan na murkushe duk wasu masu adawa da manufofinta.

Karin bayani: Mali: Tsayar da ranar zaben raba-gardama

Konate ya ce:  ''Wannan ba bakon abu ne ba daga hukumomin sojan da ke kokarin yin karar tsaye ga dokoki da 'yancin dan Adam. A yau babu wanda zai yi kasadar yin magana a game da abin da ke faruwa a Mali domin alkalai sun zama 'yan amshin shatan wadannan sojojin da suke  tunanin kama-karya ce hanya mafi a'ala ta gudanar da mulki.''

Me ra'ayin masu fafutuka kan wannan batu?

Masu fafutuka sun ki ce uffan game da rusa kungiyar daliban Mali
Masu fafutuka sun ki ce uffan game da rusa kungiyar daliban MaliHoto: Getty Images/M. Cattani

Tun bayan da gwamnatin mulkin sojan Mali ta fara bai wa gawa kashi don mai rai ya ji tsoro, masu fafutuka a kasar sun yi gum da bakinsu don gudun fushin fadar mulki ta Bamako. Misali duk 'yan kungiyoyin da muka yi kira domin tsokaci kan wannan batu, sun bukaci da a sakaya sunansa, lamarin da ke haifar da dumuwa kan makomar 'yancin fadar albarkacin baki a kasar ta Mali.