An soki lamirin batagarin yan siyasa a Nigeria | Labarai | DW | 09.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soki lamirin batagarin yan siyasa a Nigeria

Hukumar kare hakkin bil adama ta Human Right Watch ta soki lamirin batagarin yan siyasa a Nigeria, da cewa sune suke lalata rayuwar matasa a kasar. Hukumar tace batagarin yan siyasar na yin amfani da matasan ne, a matsayin yan daba da yan banga a lokacin da suke fafutikar neman madafun iko.Ire iren wadannan matasa a cewar hukumar ta Human Right Watch, na amfani da makamai da makaman tansu, don ba da kariya ga iyayen gidan nasu a lokacin yakin neman zabe. Hakan a cewar hukumar na kawo yamutsi da tashe tashen hankula, wanda kann kai ga asarar rayuka.Har ilya yau Human Right Watch ta kuma soki batagarin yan siyasar da daurewa cin hanci da rashawa gindi,ta hanyar ba da na goro domin a zabe su.