1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu wasan sada zumunta tsakanin Isra'ilada Argentina

Abdourahamane Hassane
June 6, 2018

Isra'ila ta bayyana takaicinta bayan da aka soke karawar kwallon kafa ta sada zumunta da aka shirya yi tsakanin Isra'ila da Agentina a birnin Kudus a ranar Asabar mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2z20G
Argentinien Lionel Messi, Fußballspieler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. R. Caivano

An dai soke wasan na sada zumunta a kan matsin lambar da Faladinawa suka yi a kan Lionel Messi cewar kada ya shiga wasan,domin martaba dubban magoya bayansa falasdinawa musulmi, wanda Isra'ila ke yi wa kashin mumuke kamar yadda suka bayyana. Ministan tsaro na Isra'ila Avigdor Lieberman, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar soke wasan abin takaici ne.