An shiga kada kuri′a a zaben kasar Girka | Labarai | DW | 25.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An shiga kada kuri'a a zaben kasar Girka

Neman a yafewa kasar ta Girka kudaden da aka bata bashi na zama abinda ke jan hankulan al'ummar wannan kasa, abin da kuma jam'iyyar Syriza ke cewa na cikin manyan abinda tasa a gaba.

Al'ummar kasar Girka sun fita tashoshin kada kuri'a a yau Lahadi,cikin wani muhimmin zabe da aka dade ana jimiransa. Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a dai tun da fari ta nuna cewar jam'iyyar Syriza zata iya samun nasara kan jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya da Firaminista Antonis Samaras.

Jam'iyyar dai ta Syriza ta sha alwashin samar da sauyi ga shirin tallafawa kasar ta Girka dan ta samu ta fita daga matsalar tattalin arziki da kasashen Turai ke yi, inda take son kawo karshen duk wasu sharuda masu tsauri.

A bangaren kasashen da ke bin kasar basuka kuwa na ganin batun yin afuwa ma bai tasoba.