An sanya dokar ta baci a Tafkin Chadi
May 8, 2026
Ayyana dokar ta baci a Tafkin Chadi na zuwa ne kwanaki bayan da mayakan Boko Haram suka kashe jami'an soji a kalla 24 a wani sansanin soji da ke Barka Tolorom. Dokar ta bacin za ta fara aiki ne daga daren 7 zuwa daren ranar 27 ga watan Mayun 2026. Hukumomin sun ce za a rufe iyakar kasar tare da sanya dokar hana zirga-zirga.
Karin bayani: kasar Chadi ta shiga rudani bayan harin Boko Haram
A sakon da ya gabatar ta kafar talabijin din kasar, mai magana da yawun gwamnatin Chadi, Gassim Cherif ya ce, daukar wannan matakin zai saukaka musu wajen kama wadanda ake zargi da kai harin da kuma hana kai kawon mutane da motoci da mashina. Yankin na Tafkin Chadi da ya hada iyakar kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da Chadi ya sha fama da matsaloli na mayakan Boko Haram, inda suke zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan.