1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da ranar zaben Aljeriya

April 10, 2019

Hukumomi a Aljeriya sun bayyana ranar da al'umar kasar za ta fita don kada kuri'un zaben wanda zai shugabancin kasar bayan kawo karshen shugabancin shugaba Bouteflika.

https://p.dw.com/p/3Ga07
Algerien Abdelkader Bensalah
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Fadar shugaban kasar Aljeriyar ce ta bayyana ranar Alhamis hudu ga watan Yulin bana, a matsayin ranar da za a gudanar da zabe shugaban kasa. Cikin wata sanarwar da aka fitar a wanna Laraba, fadar ta Aljeriya ta tabbatar da hakan. 

A ranarTalata ne kuwa shugaban rikon kasar na yanzu, Abdelkader Bensalah, ya yi alkawarin sama wa al'umar kasar zabe mai tsafta.

Makonni da dama ne dai al'umar kasar ke ta zangar-zangar adawa da shugabancin kasar, da ta kai ga murabus din tsohon shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ya shafe shekaru 20 bisa karaga.

Bisa tsari dai kwanaki 90, Shugaba Abdelkader Bensalah zai yi, kafin ya mika wa sabuwar gwamnati mulki.