1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu raguwar makaman nukiliya a duniya

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2018

Wani rahoto da cibiyar SIPRI mai bincike kan zaman lafiya a duniya ta fitar ya nunar da cewa adadin makaman nukiliya ya ragu a duniya a shekara ta 2017.

https://p.dw.com/p/2zmy1
Symbolbild Atombombe
Hoto: Getty Images/AFP/F. Naeem

Sakamakon wani rahoton bincike kan yaduwar makaman nukiliya a duniya da aka wallafa a wannan Litinin ya nunar da cewa adadin harsashen nukiliya da ke da akwai a duniya ya ragu zuwa dubu 14, 465 a farkon shekara ta 2017. 

Rahoton wanda cibiyar SIPRI mai bincike kan batun zaman lafiya da ke da cibiyarta a birnin Stokholm na kasar Sweden ya ce an samu ragowar harsashen nukiliyar 470 idan aka kwatanta da adadin da ke da akwai a farkon shakarar 2017. 

Cibiyar ta SIPRI ta ce ragowar da aka samu ta yi daidai da tanadin yarjejeniyar rage makaman nukiliya da aka cimma a shekara ta 2010 tsakanin kasashen Rasha da Amirka wadanda su biyu ke mallakar kaso 92 cikin dari na makaman nukiliya da ke da akwai a duniya a yau. 

Sai dai rahoton cibiyar ta SIPRI ya ce a daidai lokacin da suke rage yawan makaman nukiliyar nasu da ke ajiye, manyan kasashen duniyar da suka mallaki makamin nukiliyar na ci gaba da ware makudan kudade wajen kera sabbin makamai na zamani da suka fi hadari.