An samu fashewar bam a kasuwar Bauchi | Labarai | DW | 22.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu fashewar bam a kasuwar Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya na cewar bam ya tashi a babbar kasuwar jihar wanda ke kan gaba wajen samun cinkoson mutane.

Masu aiko da rahotanni suka ce tashin bam din ya yi sanadin rasuwar mutane da damalalata dukiya ta miliyoyin Naira. Ya zuwa yanzu dai ba a tantance yawan wanda wannan tashin bam din ya hallaka sai dai ana hasashen wanda suka rasu ka iya yin yawa saboda cinkoson da kasuwar ke da shi.

Babu dai wanda ya dau alhakin kai wannan hari wanda ke zuwa sa'o'i kalilan bayan da wani bam din ya tashi da safiyar Litinin a tashar Dukku da ke jihar Gombe da ke makotaka da jihar ta Bauchi inda nan ma aka samu asarar rayuka.