An sami asarar rayuka a Kenya | Labarai | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami asarar rayuka a Kenya

Akalla mutane hudu sun mutu, bayan rikicin samun sakamakon farko na zaben shugaban kasa a jiya Laraba.

Rahotannin da ke fitowa daga Nairobi babban birnin kasar Kenya, na cewa akalla mutane hudu ne aka tabbatar sun mutu, bayan rikicin samun sakamakon farko na zaben shugaban kasa a jiya Laraba. Hukumar zaben kasar ta bayyana shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda kuri'unsa suka fi yawa a galibin kuri'un da aka kidaya. Jagoran adawar kasar Raila Odinga ya yi zargin kutse a na'aurorin hukumar zaben kasar, da kuma ya ce ba zai lamunta da shi ba, lamarin da ya tunzura magoya bayansa nuna fushi a sassan kasar a jiya Laraba.

Gabanin zaben dai an kashe wani babban jami'in hukumar zaben mai kula da sashen adana bayanai, wanda kuma wasu suka ce ba zaii rasa nasaba da zafin zaben ba. Bayanai sun ce 'yan sandan kasar sun yi amfani da karfi musamman ma buda wuta a kan masu zanga-zangar.