An samar da irin wake mai jure fari a Yuganda | Sauyi a Afirka | DW | 27.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

An samar da irin wake mai jure fari a Yuganda

Matsalar sauyin yanayi da cututtuka da ke barazana ga irin wake, shi ya sa masana kimiyya na cibiyar nazarin harkokin noma suka bullo da hanyar wadata al'umma da abinci.

Florence Nakasumba mai shekaru 55 da haihuwa ta girbi amfanin noma a lambunta da ke gundumar Masaka a tsakaiyar kasar Yuganda. Duk da cewa tana daga cikin kananan manoman kasar, amma ta ce amfani da irin wake da ke jure wa fari ya sawwake aikinta da noma tare da samar amfanin mai yawa.

"Wannan wake na da kyau mai, iri daya kawai ake bukatar shukawa. Da wuri ne ake shukashi, kuma dole a tabbatar da cewa an sare ciyayin da ke mamaye su a kalla sau uku."

Gyara nau'o'in waken don aikashi kasuwa na daya daga cikin ayyukan da kamfanin Pearl Seeds ya sa a gaba. Daraktan kanfanin Richard Masagazi ya ce bukatar da ake nuna wa wannan nau'i na waken da aka bunkasa na dada karuwa a cikin Yuganda.

"A cikin wannan kakar, mun sayar da kimanin ton 250 zuwa 300 na waken, kuma mun riga mun sayar da wasu wake a yankunan yammacin Nilu inda muke da 'yan gudun hijirar Sudan, mutane da yawa ne bukatarsa amma ba su san yadda za su zo su sameshi ba."

Duk da cewa ana matikar bukatar waken da aka bunkasa kwayoyin halittarsa a makarantun Yuganda, amma kuma ba a cika samunsu cikin sauki ba. Gabriel Luyima na daya daga cikin masana kimiyyar albarkatun gona da suka samo irin nau'o'in wake da aka fi sani da NABE 23 .

"Muna da dalilan da ya sa muka bunkasa kwayoyin halittar wannan wake, shi ne matsalar cututtuka da ke lalata wake, don haka manoma suna samun matsaloli masu yawa wajen samun amfanin gona. Dalili na biyu kuma shi ne akwai wuraren da sauran wake ba zai iya tsirowa ba musamman a yankunan da yashi ke da yawa kuma ba sa tsotse ruwa sosai."

Gwamnatin yuganda ta nuna farin cikinta dangane da irin wannan nau'in na waken da kwararru suka samar. Kwamishinan da ke kula da 'yan gudun hijirar Kazungu David Apollo, ya ce wadannan na'o'in waken za su ci ke gibin da ake da shi a fannin wake tare da magance matsalar karancin abinci da yawancin 'yan gudun hijirar da suka kimanin miliyan 1 da dubu 400 ke fama da ita.

"Samar da wadataccen abincin da ake bukata, wata manufa ce da gwamnati ta ke ganin cewa ya dace a zuba jari a ciki, don tabbatar da cewa an ceto rayukan wadannan mutane da ke neman mafaka. Saboda haka ne muke maraba da nau'in wake NABE. Mun ga taimakon da ya kawo a yankin Nilu na yamma, kuma muna jin cewa irirn wannan mataki ne zai iya  magance matsalar rashin abinci mai gina jiki."

Dama dai wake na daga cikin na'in abinci mai gina jiki da 'yan Yuganda suka dogara da su a kasar Yuganda.