1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An saki dukkan daliban Kuriga da aka sace a Najeriya

March 24, 2024

Gwamnan jihar Kaduna a tarayyar Najeriya Sanata Uba Sani ya sanar da cewa an saki dukkan daliban nan kimanin 287 da ’yan bindiga suka sace a kauyen Kuriga dake jihar.

https://p.dw.com/p/4e48Y
Dandazon mutanen Kuriga a yayin da suke maraba da shigowar jami'an 'yan sanda a kwanakin baya.
Dandazon mutanen Kuriga a yayin da suke maraba da shigowar jami'an 'yan sanda a kwanakin baya.Hoto: AP/dpa/picture alliance

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ofishin gwamnan ne ya fitar da sanarwar sakin daliban na Kuriga a safiyar yau lahadi. Kazalika Gwamnan ya kuma wallafa sanarwar dukkan daliban a shafinsa na Facebook inda yace babu wani abu na cutarwa da ya same su.

Karin bayani: Kaduna: Ko daliban da aka sace za su tsira?

Kusan kwanaki 16 kenan da mahara dauke da muggan makamai suka kwashe daliban a makarantun furamare da sakandare a kauyen na Kuriga lamarin da ya tada hankalin mutane a ciki da wajen  Najeriya.

Karin bayani:  Tinubu ya yi watsi da biyan kudin fansa ga 'yan fashi