1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake zargi Rasha da kutsen internet

Gazali Abdou Tasawa
October 4, 2018

Kasashen Birtaniya da Ostareliya sun zargi hukumar leken asirin sojan kasar Rasha da yin kutsen yanar gizo a hukumomi da kungiyoyi a kasashe da dama.

https://p.dw.com/p/35wsE
Russland St. Petersburg Vladimir Putin
Hoto: picture-alliance/AP Photo/D. Lovetsky

Kasashen Birtaniya da Ostareliya sun zargi hukumar leken asirin sojan kasar Rasha da yi wa wasu hukumomin siyasa da na wasannin motsa jiki da kamfanoni da kuma kafafan yada labarai na kasashen duniya da dama kutse ta hanyar yanar gizo ta hanyar amfani da wasu shahararrun shafukan masu kai hari ta yanar gizo.

 A cikin wata sanarwa da ministan harakokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya fitar a wannan Alhamis ya bayyana kasar Rashar da bijire wa dokokin kasa da kasa da aikata ba daidai ba ba tare da la'akari da abin hakan ka iya haifarwa ba zaman lafiyar duniya. 

Ministan ya ce babu makawa su da sauran kasashen kawayensu za su mayar wa da hukumar leken asirin sojan kasar ta Rasha da martani kan wannan harin yanar gizo wanda ya ce ya haddasa asarar miliyoyin Dala ga kasashe da dama.