1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kashe wasu sojoji a arewacin Kamaru

July 27, 2021

Wani sabon hari a kan dakarun kasar Kamaru, ya yi sanadin salwantar mayakan kasar da ma jikkatar wasu. Karo na biyu ke nan cikin mako uda da ake kashe sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/3y9E3
Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule
Hoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

Wasu mahara da ba a kaiga tantace su ba, sun kashe sojojin Kamaru biyar da ma wani farar hula guda a wani hari da suka kai kan shingen binciken sojojin da ke yankin arewa mai nisa.

Jami'ai a yankin da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce 'yan bindigar sun shiga wani kauye ne da ake kira Zigue a daren Talata, sannan suka tafka wannan ta'asa.

Wannan ne dai karo na biyu da ake kai hari a yankin arewan mai nisa a Kamaru, bayan wani da aka kai yankin Fotokol a karshen mako.

Kasar ta Kamaru da makwabtanta irin su Najeriya da Chadi na fama da hare-hare daga Boko Haram da ma na baya-bayan na reshen IS da ke kiran kansa ISWAP a takaice.