An sake bude kasuwar kirisimeti ta Berlin | Labarai | DW | 22.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake bude kasuwar kirisimeti ta Berlin

An sake bude kasuwar kirisimeti ta Berlin a daidai lokacin da jami'an tsaron Jamus ke ci gaba da neman Anis Amri da ake zargi da kai hari ruwa a jallo.

Jami'an 'yan sanda Jamus sun yi dirar mikiya a birnin Dortmund a gidajen wasu da ke da alaka da dan asalin Tunisiyan nan da ake zargi da kai hari a kasuwar Kirisimeti na birnin Berlin tare da cafke hudu daga cikinsu. Tuni aka sake bude kasuwar kirisimeti ta birnin Berlin kwanaki uku bayan kai wannan harin. Sannan kuma ana ci gaba da farautar dan asalin Tunisiyan a duk fadin Turai.

Jaridar New-York Time ta bayyana cewar akwai yiwuwar Anis Amri ya taba samun alaka da kungiyar IS. Sannan ya sami bayanai kan yadda ake hada bama-bamai a kafofin sadarwa na internet. Jami'an gwamnatin Jamus sun yi tayin bayar da tukuwcin Euro dubu 100 ga duk wanda ya bayar da labarin yadda za a kama shi. Tuni dai dan uwansa mai suna Abdelkader da ke kasar Tunisiya ya nuna takaicinshi game da abin da ya faru.

"Ina cikin bakin ciki kamar duk wani dan Tunisiya game da abin da ya faru. Lokacin da 'yan sanda suka zo har gida suka dauki mahaifiyata ne muka san abin da ake ciki. Mun zo garinmu Ouslatia ne takanar dangane da wannan batu. a Tunis muke da zama."