1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An saka ranar zabukan Togo bayan shiga rudanin siyasa

April 10, 2024

Gwamnatin Togo ta saka ranar 29 ga watan Afrilu a matsayin ranar zaben 'yan majalisun dokokin da na yankuna bayan rudanin siyasa da kasar ta fada sakamakon dage zabukan da kuma kwaskware kudin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/4ebNn
Wahlen in Togo Flagge
Hoto: AP

Gwamnatin kasar da ke yammacin Afrika ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fidda da maraicen ranar Talata bayan kamalla wani zama tattauna da majalisar ministoci.

Karin bayani: Togo: 'Yan adawa sun kira bore kan dage zabe

Bugo da kari fadar mulki ta Lome ta sanar da haramta duk wani jerin gwano a fadin kasar tana mai yin kashedi ga kawancen jam'iyyun adawa da ya kira zanga-zanga a ranakun Juma'a da Asabar masu zuwa domin kalubalantar matakin dage zabukan.

Har kawo wannan lokaci 'yan adawan Togo ba su yi wani martani a game da tsayar da ranar zabukan ba wadanda tun da farko aka tsara gudanar da su a ranar 20 ga wannan wata na Afrilu.