Togo: ′Yan adawa sun kira sabuwar zanga-zanga | Labarai | DW | 26.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Togo: 'Yan adawa sun kira sabuwar zanga-zanga

'Yan adawar kasar Togo sun yi kira ga wasu sabbin jerin zanga-zanga da za su gudanar a kasar a yunkurin da suke na nuna adawarsu ga matakan shugaban kasar Faure Gnassingbe.

A cikin wata sanarwa ce da suka fitar, gamayyar jam'iyyu 14 na 'yan adawar kasar ta Togo suka yi kira ga 'yan kasar da su fito dafifi domin halartar zanga-zangar a ranaikun 29 da 30 ga watan Nuwamba sannan da ranar biyu ga watan Disamba mai zuwa.

'Yan adawar na neman tirsasa wa gwamnatin ta Shugaba Faure Gnassingbe komawa ga kundin tsarinn mulki na 1992 wanda ya tanadi kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa, inda suka yi Allah wadai da muzgunawar da hukumomin ke yi musu ta hanyar amfani da jami'an tsaro na kasa.

Tun daga karshen watan Augusta 'yan adawar kasar ta Togo ke shirya zanga-zanga tare ma da neman shugaban kasar da ya gaji mahaifinsa wajen shugabancin kasar da ya yi murabus.