1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace wani baturen Sweden a Najeriya

Ramatu Garba Baba
August 9, 2021

Mutum guda ya mutu a yayin wani artabu a tsakanin 'yan bindiga da suka sace wani dan kasar Sweden a jahar Ogun da ke kudancin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3yjfO
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Rundunar tsaro ta 'yan sandan jahar Ogun a Najeriya, ta ce, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani bature dan kasar Sweden da kuma wani mutum guda dan Najeriya a jahar ta Ogun da ke Kudancin kasar. Mutum guda ya rasa ransa a yayin musayar wuta a tsakanin 'yan bindigan da tawagar wadanda aka sacen, kafin daga bisani su yi nasarar yin awon gaba da mutanen biyu. 

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jahar, ya ce lamarin ya faru ne a yayin da tawagar da ke yiwa baturen rakiya suka ziyarci wata gonar kiwon dabbobi a yammancin ranar Asabar din da ta gabata. Matsalar satar mutane dai don neman kudin fansa na kara yin kamari a Najeriya.