An rantsad da sabon sakatare janar na MDD a birnin New York | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsad da sabon sakatare janar na MDD a birnin New York

An rantsad da dan kasar KTK nan Ban Ki Moon a matsayin sabon babban sakataren MDD a wani buki da aka yi a birnin New York. Ban Ki Moon mai shekaru 62 a duniya ya yi alkawarin zama jagora na gari ga gamaiyar ta kasashen duniya tare da yin aiki a matsayin wani mai dinke baraka tsakanin kasa da kasa. A ranar daya ga watan janeru Ban zai karbi ragamar shugaban MDD daga magabacinsa Kofi Annan. Wani zama na musamman da babbar mashawartar majalisar ta yi a yau ta karrama sakatare janar din mai barin gado Kofi Annan. Jakadun kasashe daban daban sun yaba masa bisa jagorantar majalisar a wani mawuyacin lokaci na yi mata kwaskwarima.