An rantsad da majalisar ministoci a ƙasar Thailand. | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsad da majalisar ministoci a ƙasar Thailand.

Sarki Bhumibol Adulyadej na ƙasar Thailand ya rantsad da sabbin ministocin da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta naɗa, makwanni uku bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi. Majalisar ministocin dai za ta yi mulki ne har tsawon shekara ɗaya, kafin gudanar da zaɓe cikin watan Oktoba na shekara ta 2007. Manyan masana tattalin arzikin ƙasar da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati da kuma tsoffin manyan hafsoshin soji guda biyuna na cikin waɗanda aka naɗa a muƙaman ministocin. Kafin dai a rantsad da minsitocin yau, sai da Friamiya Surayud Chulanont, ya miƙa jerin sunayensu ga fadar sarkin don samun amincewarsa.