An nemi Isra′ila ta dakatar da gina matsugunai | Labarai | DW | 06.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi Isra'ila ta dakatar da gina matsugunai

Gwamnatocin Faransa da Jamus da Italiya da Spain da kuma Birtaniya sun bukaci Isra'ila da ta dakatar gina sabbin matsugunai da ta fara shirin yi a gabar yamma ta Kogin Jordan.

A wani sako na hadin gwiwa da kasashen suka fidda a wannan Alhamis din, sun ce gina sabbin matsugunan musamman ma a yankin nan Har Homa da ke tsakanin Gabashin Jerusalem da Bethelehem, ba abin da zai haifar illa jawo nakasu ga kokarin da ake yi wajen samar kasar Falasdinu.

Kimanin gidaje dari biyar da arba'in ne dai mahukunta Isra'ila suka dauki aniyar ginawa a Gabar Yamma ta Kogin Jordan din da suke mamaye da ita, kuma mafi akasari irin wannan yunkuri kan haifar da cece-kuce tsakaninsu da Falasdinawa.