An nemi hada karfi domin magance matsalar fyade | Siyasa | DW | 11.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An nemi hada karfi domin magance matsalar fyade

Ana ci gaba da neman kawo hanyoyin shawo kan cin zarafin mata musamman a yankunan da ake samun tashe-tashen hankula

A birnin London kasar Britaniya ana taron kolin duniya kan yaki da mummunar dabi'ar yin fyade a wuraren da ake rikici. Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague tare da jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya domin yaki da dabi'ar fyade, Angelina Jolie suke daukar bakuncin taron na birnin London.

Taron na yini hudu shi ne irinsa na farko da aka taba gudanarwa, bayan matsa kaimi tsawon shekaru biyu Birtaniya, ta dauki alkawarin ci gaba da wannan fafutuka ta yaki da fyade a matsayin makamin yaki. Yayin da kungiyoyi daga masu zaman kansu ke cewa za su bayar da duk gudumawar da ta dace.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar a taron ta nuna cewa ba a nahiyar Afirka kadai ake fama da wannan matsala ba, amma matsala ce da ta zame ruwan dare game duniya a duk yankunan da ake fama da rikice-rikice. Haka kuma an kiyasta cewa a kasar Jamhuriyar Demokaradiyya Kwango ke kan gaba wajen fama da matsalar. A lokacin yakin kasar Bosniya da ke nahiyar Turai, an kiyasta mata sama da dubu hamsin da suka galabaita a hannun mayaka. Lokacin kisan gillar kasar Ruwanda kuwa mata kusan rabin milyan suka tagayyara ta wannan mummunar dabi'a.

Mawallafi: Sani Dauda
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin