An nada mai bincike kan huldar Trump da Rasha | Labarai | DW | 18.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada mai bincike kan huldar Trump da Rasha

Amirka ta Robert Mueller tsohon daraktan hukumar leken asiri ta kasa FBI, domin gudanar da bincike a kan zargin da ake na wata huldar tsakanin wasu na hannnun damar Shugaba Trump da kuma kasar Rasha. 

Mahukuntan shari'a a Amirka sun nada Robert Mueller da ke zama tsohon daraktan hukumar leken asiri ta kasa wato FBI, domin gudanar da bincike a kan zargin da ake na wata huldar kut da kut da ke da akwai tsakanin wasu na hannnun damar Shugaba Trump da kuma kasar Rasha. 

 Mueller mutun ne da ya riki mukamin daraktan hukumar leken asiri ta kasa ta FBI daga shekara ta 2001 zuwa 2013  tun daga lokacin gwamnatin George W. Bush har zuwa ta Barack Obama.

Ya na da kima a idon Amirkawa na a matsayin wani mataki na neman rage katsalandan din da gwamnatin kasar ke yi a cikin ayyukan binciken da hukumar ta FBI ke yi kan wannan batu na kusancin wasu na hannun damar Shugaba Trump da kasar Rasha. 

Sai dai da yake mayar da matrani ta shafinsa na tweeter kan nadin tsohon daraktan hukumar ta FBI Shugaba Trump ya ce ba shi da wata fargaba a game da sakamakon da binciken zai bayar domin yana da tabbacin babu wata alakar da ke da akwai tsakanin wasu na hannun damar tasa da kasar Rasha.