An mayar da kasar Qatar saniyar ware | Siyasa | DW | 06.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An mayar da kasar Qatar saniyar ware

Matakin da manyan kasashen Larabawa suka dauka na mai da kasar Qatar saniyar ware kan zarginta da goyan bayan ta'addanci na kara jefa al'ummar Larabawan cikin garari.

Birnin Doha,babu saukar jiragen sama daga Saudiya da Yemen da Masar da dai sauran su

Birnin Doha,babu saukar jiragen sama daga Saudiya da Yemen da Masar da dai sauran su

Kasashn shida da suka yanke hulda da Qatar din kan zargin tallafa wa aiyukan ta'addanci a yankin, su ne Saudiyya da Masar da Daular Larabawa da Bahrain da Kuwaiti da Yemen gami da yankin da ke karkashin ikon Janar Khalifa Haftar da ke gabashin Libiya. Tuni dai kasashen Kuwaiti da Sudan da ma Turkiyya suka nuna aniyarsu  ta shiga tsakanin bangarorin biyu, don kwantar da hankula da kuma sassantawa. To sai dai kamar yadda Fahad Shahami, wani mai fashin baki a Saudiyya ke gani, zai yi wuya a sassanta, muddin Qatar ba ta sauya tafiyarta ba.

Jama'a a Qatar na kokarin sayan kayan abinci,saboda matakin da kasashen Laabawan suka dauka

Jama'a a Qatar na kokarin sayan kayan abinci,saboda matakin da kasashen Laabawan suka dauka

  "Siyarar da Qatar ke bi, shi ne dalilin mayar da ita saniyar ware, kasancewarta karamar kasa, ba za ta iya yin tasiri a Yankin Gabas ta Tsakiya ba, sai ta hanyar hada kai da 'yan ta'adda irin su kungiyoyin Hamas da Hizbullah, da kuma Iran. Zai yi wuya kasar ta iya rabuwa da 'yan ta'adda, muddin dai ba kifar da wadannan sarakunan da ke renon ta'addanci aka yi ba.”

Wannan matakin da ke ci gaba da janyo cece-kuce tsakanin al'ummar Larabawa dai na zuwa ne mako guda bayan ziyarar da shugaban Amirka Donald Trump ya kai kasashen Saudyiya da Isra'ila, ziyarar da ta kai kasashen ga kulla sabon kawancen yaki da ta'addancin da suka ce shi ne babbar barazanar tsaro da yankin ke fuskanta.

Sauti da bidiyo akan labarin