An kusa kawo karshen rikici a kan karin albashi a Najeriya | Siyasa | DW | 12.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kusa kawo karshen rikici a kan karin albashi a Najeriya

An kama hanyar kai karshen rikicin karin albashin ma'aikata da aka dade ana yi a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta ce ta kafa kwamitin da zai kammala aiki bisa sabon albashin.

Duk da cewar dai tun cikin watanni biyar da suka wuce Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu bisa dokar karin albashin, ana shirin kare shekarar bana cikin halin ja-in-ja tsakanin ma'aikatan kasar da ke zargin mahukunta da jan kafa,da kuma gwamnatin da ke cewar an kusa kawo karshe. Baki dai ya zo daya tsakanin gwamnati tarayyar da jihohi dama kungiya ta masu daukar aikin game da sabon mafi karancin albashin Naira 30,000. Abin jira a gani dai na zaman kaiwa ga murmushin ma'aikatan tarrayar Najeriyar da ke zaman na baya ga dangi a cikin yanki na yammacin Afirka a kan batun albashin.

Sauti da bidiyo akan labarin