An ceto daliban jami'ar Gusau biyar daga hannun 'yan bindiga
March 17, 2024Talla
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da kubutar da dalibai biyar daga cikin 15 da 'yan bindiga suka sace a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Mustafa Jafaru Kaura ya shaida wa wakilin DW Yuusf Ibrahim Jargaba cewar akwai wasu karin mutanen da gwamnati ta kubutar tare da daliban guda biyar.
Tun watanni shida da suka gabata ne dai 'yan bindiga suka shiga jami'ar ta Gusau da ake wa lakabi da FUGUS inda suka yi awon gaba da wadannan dalibai mata. Yanzu hankali ya koma kan sauran 'yan mata 10 da ke hannun 'yan bindigar.