1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kubatar da Turawa a Kamaru

April 4, 2018

Rahotannin da ke fitowa daga Kamaru, na cewa an sako wasu 'yan kasashen Turai 12 da aka yi garkuwa da su a yankin yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2vUC6
Kamerun Minister für Kommunikation Bakary Tchiroma
Issa Tchiroma Bakary, ministan sadarwa a KamaruHoto: picture-alliance/dpa/MAXPPP/ J.-P. Kepseu

Hukumomi a kasar Kamaru sun ce an sako wasu 'yan kasashen Turai 12 da aka yi garkuwa da su a yankin yammacin kasar inda wasu ke neman ballewa don kafa kasar Ambazoniya. A cewar hukumomin, mutanen 12 da suka je yawon shakatawa, bakwai daga cikinsu 'yan kasar Switzerland ne, yayin da sauran biyar kuma Italiyawa ne.

Dakarun kasar ne suka kubutar da su daga hannun wadanda jami'an gwamnatin suka ce 'yan ta'addan yankin kudu maso yammacin kasar ne, kamar yadda ministan sadarwa Issa Tchiroma Bakary, ya tabbatar.

A share guda kuma wasu bayanan sun tabbatar da mutuwar wasu dakarun Kamarun su biyar a wani harin da 'yan bindiga suka kaddamara yankin arewa mai nisa. Sai dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin, wanda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito.