An kebe mutane a arewacin Saliyo saboda Ebola | Labarai | DW | 14.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kebe mutane a arewacin Saliyo saboda Ebola

Daruruwan mutane ne aka tantance su a yayin da cutar Ebola ta sake bulla a arewacin kasar Saliyo.

Rahotanni da ke futowa daga kasar Saliyo na nuni da cewar daruruwan mutane ne jami'an lafiyar kasar suka tantance a arewacin kasar sakamakon bullar cutar Ebola a jikin wata yarinya 'yar shekaru 16 a duniya, da ta rigamu gidan gaskiya a wani abu da ake ganin cutar na da alaka musayar cuttutukan jima'i.

A yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Freetown Emmanuel Conteth wanda ke zama shugaban cibiyar kula da masu cutar Ebolan a lardin Bombali na Saliyo, ya ce mutane 690 da ke zaune a kauyen da yarinyar ta mutu za a kwashe su daga cikin jama'a har na tsawon makonni uku don samun tantancewa.

Kana kuma tuni aka kwashi wasu mutane bakwai da ta yi mu'amala da su zuwa cibiyar tantance cutar Ebolan da aka kebe domin duba masu dauke da kwayar cutar.

Kasar Saliyo dai na daya daga cikin kasashen da cutar Ebola ta yi wa ta'adi a inda daruruwan mutane suka mutu sakamakon cutar da har yanzu ake lalubar maganinta.