An kashe ′yan sanda a Kamaru | Labarai | DW | 08.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe 'yan sanda a Kamaru

'Yan aware a Kamaru sun halaka jami'an 'yan sanda a bangaren kasar mai amfani da turancin Ingilishi, kwana guda bayan kisar wani jami'in tsaro.

Wasu 'yan aware a Kamaru sun halaka jami'an sanda biyu a sashe kasar mai amfani da turancin Ingilishi, kwana guda bayan kisan wani jami'in tsaro. Kakakin gwamnatin kasar Issa Tchiroma Bakary, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP aukuwar lamarin da ya ce ya faru ne a Bamenda.

A cewar Tchiroma Bakary, 'yan awaren sun buda wuta kan jami'an na 'Gendarmes' ne da wasu muggan makamai lokacin da suke aikin gadin wani banki. Haka nan an yi zagin maharan da yin awon gaba da makaman jami'an.

Bamenda dai shi ne gari mafi girma a yankin arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan kasar da ke fama da rikicin wariya.