An kashe wani shahararren lauya a Turkiya | Labarai | DW | 28.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani shahararren lauya a Turkiya

An kashe Diyarbakir Tahir Elci shahararren lauyan da ya yi fice wajen kare hakkin Kurdawa a lokacin wasu harbe-harben bindigogi da suka barke a birnin Sur na kudu maso gabashin kasar.

A kasar Turkiya Hukumomin tsaro da na kiwon lafiya sun tabbatar da mutuwar wani shahararren lauya na kasar mai suna Diyarbakir Tahir Elci da ya yi fice wajen kare hakkin Kurdawa. Lamarin ya wakana ne a lokacin wani harbe-harben bindigogi da ya wakana a garin Sur birnin mafi girma na kudu maso gabashin kasar ta Turkiya inda Kurdawa suka fi rinjaye.

Ko baya ga lauyan, wani dan sanda ya rasa ransa yayin da wasu mutane 10 daga ciki har da wani dan jarida suka ji rauni. An kashe lauyan ne jim kadan bayan da ya kammala wani taron manema labarai a gaban wani masallacin birnin na Sur birnin da ya yi kaurin suna wajen fadace-fadace tsakanin matasa masu goyan bayan jam'iyyar PKK da kuma 'yan sanda.

A wani jawabi da ya gabata a garin Burhaniye na yammacin kasar Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya nuna alhini da bakin ciki kan lamarin inda ya ce wannan hadari na nuni da cewa yaki da ta'addanci ya dace.