An kashe sojojin Amirka guda biyu a yammacin Iraqi. | Labarai | DW | 15.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Amirka guda biyu a yammacin Iraqi.

Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqi, ta tabbatad da rahotannin da ke nuna cewa, sojojinta guda biyu ne sukka sheƙa lahira, a wani ɗauki ba daɗin da wani rukunin dakarun Amirkan suka yi da `yan tawaye a jihar Al Anbar da ke yammacin ƙasar.

Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirka da suka rasa rayukansu a Iraqin, tun da aka afka wa ƙasar shekaru uku da suka wuce, ya kai dubu 2 da dari 3 da 9, bisa wasu alƙasluman da ma’aikatar tsaron Amirkan wato Pentagon ta buga.