An kashe Qurdawa yan tawaye a Turkiya | Labarai | DW | 30.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Qurdawa yan tawaye a Turkiya

Rundunar sojin kasar turkiya tace Qurdawa yan tawaye sun kai hari kann wata motar soji inda suka kashe mutane 12 .Jamian kasar sun sanarda cewa membobin jamiyar PKK suka kai hari kann motar sojojin dauke da mutane 14 kusa da bakin iyaka kasar da Iraq.Mutane biyu sun tsira da raunuka inda yanzu haka suke asibiti.Wannan hari dai ya biyo bayan kashe wani shugaban kungiyar ce a lardin.Kungiyara awaren ta Qurdawa ta fara harkokinta ne a 1984 tare da nufin kafa kasar Qurdawa a kudu maso gabacin Turkiya.Fiye da mutane 30,000 suka rasa rayukansu cikin wannan rikici.