1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Harin yan bindiga ya hallaka jama'a

Abdoulaye Mamane Amadou
July 10, 2021

Rundumnar 'yan sandan Najeriya ta ce adadin wadanda suka hallaka sakamakon harin 'yan bindiga a Jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin kasar sun kai 35.

https://p.dw.com/p/3wJ8W
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Shedu sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP da cewa, wadanda suka hallaka sun haura mutun 40, baya ga wasu bakwai da ke kwance a gadon asibiti a yayin hare-haren da 'yan fashin dajin suka kai kan kauyuka biyar na jihar ta Zamfara.

Wanannn lamarin na zuwa ne a yayin da ko a ranar Larabar da tagabata, wasu 'yan fashin daji suka hallaka mutun takwas a kauyen Tsauwa da ke jihar Katsina mai makwaftaka da Zamfara, yankunan da matsalar sace-sacen jama'a da garkuwa da daliban makarantu don neman kudin fansa ke ke kara ta'azzara.