An kashe mutane kusan 20 a jihar Benue
April 24, 2018Talla
Wasu mahara da ba a tantance su ba, sun kai hari kan mazauna kauyen Ayar- Mbalong da ke karamar hukumar Gwer-East cikin jihar Benue, inda suka kashe akalla mutane 19, ciki har da wasu Limaman coci biyu.
Basaraken gargajiya da ke kauyen Mr. Ayua Daniel Abomtse, ya tabbatar wa wakilinmu Abdullahi Maidawa Kurgwi ta wayar tarho yadda lamarin ya auku.
Kokari da wakilin mu ya yi don samun karin bayani daga rundunar 'yan sandan jihar Benue lamarin ya ci tura, to sai dai wata majiya ta ce mutanen kauyen suna kan gudu zuwa neman mafaka a kauyuka mafi kusa don tsira da rayukansu kasancewar har zuwa wannan lokacin, babu isassun jami'an tsaro a yankin.