An kashe mutane bakwai a Mombasa | Labarai | DW | 28.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane bakwai a Mombasa

Wasu gungun 'yan bindiga, da ake zargi da kasancewa 'yan kungiyar MRC, sun kai hari a wani wurin shakatawa dake yankin Milindi, dake birnin Mombasa - Kenya.

A kalla mutane bakwai ciki har da jami'in dan sanda guda ne, aka bindige har lahira da sanyin safiyar wannan alhamis. Mutanen dai sun gamu da ajalinsu a lokacin da wasu gungun 'yan bindiga suka afka wa wurin shakawa da suke a wani yanki na birnin Monbasa da ake kira Milindi a Kenya. Babban jami'in 'yan sanda dake yankin Aggrey Adoli ya shaidar da cewar an kashe shida daga cikin masu kai harin, a yayin da jami'in dan sanda guda ya rasa ransa. A cewar sa dai, masu kai harin 'yan wata kungiyar tsiraru ne da ake kira MRC dake Monbasa. Milindi, yankin da wannan hari ya auku dai, na samun 'yan yawon bude ido daga kasashen ketare masu yawa, kuma nada tazarar km 95 daga birnin Mombasa dake arewacin Kenya.

Mawallafiya: Zainab mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman