An kashe mutane 20 a Filato | Labarai | DW | 16.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane 20 a Filato

Rahotanni daga birnin Jos da ke tsakiyar Najeriya, na cewa maharan sun kai hare-haren ne a ranakun Lahadi da kuma yau Litinin, inda suka kashe mutane sama da 20, tare da jikkata wasu a kauyukan karamar hukumar Bassa.

'Yan bindigan sun farawa mutanen kauyukan wadan ke neman mafaka a wata makarantar firamare cikin masarautar Irigwe. Kawo yanzu dai babu cikkakun bayanan jamai'an tsaro kan adadin mutane da suka mutu a harin, amma dai gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana zirga zirgar a karamar hukumar ta Bassa daga karfe shida na yammaci zuwa shida na safiya.