An kashe mayakan Boko Haram a Najeriya | Labarai | DW | 10.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mayakan Boko Haram a Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta ce mayakanta sun kashe 'yan kungiyar Boko Haram guda16, kana su kuma a bangaransu sun samu asarar rayuka na sojoji guda biyu.

Hakan kuwa ya biyo bayan farmakin da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai a garin Rann da ke cikin karamar hukumar Kalabalge cikin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabshin Najeriya, wanda ke kan iyaka da Kamaru. Masu aiko da rahotannin sun ce mayakan na Boko Haram sun shiga garin ne na Rann a kan babura inda suka bude wuta a kan mai uwa da wabi.Kafin daga bisanni su yi yunkurin kai hari a kan wani sanssanin soji sai dai sojojin Najeriya suka taka musu birki. Yanzu haka jama'a da dama mazauna garin na Rann, sun tsere zuwa Kamaru domin samun mafaka bayan afkuwar wannan hari.