1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe masu zanga-zanga a Bangladesh

April 17, 2021

Rahotanni daga Bangladesh na cewa mutum biyar ne suka mutu yayin da gommai suka jikkata bayan 'yan sanda sun bude wuta ga zanga-zangar neman a biya su hakokinsu.

https://p.dw.com/p/3sBCB
Bangladesh China Unruhe Protest
Hoto: AFP

Hukumomi na cewa jami'an 'yan sandan sun bude wuta ga masu zanga-zanga dubu 2 biyo bayan jifan da suke yi wa jami'an kamfanin makamashin kwal da ke kudu maso gabashin birnin Chittagong yayin da wasu suka cinna wuta ga bangarori daban daban na kamfanin. Tuni dai jami'an suka ce suna dukkan me yiwuwa wajen shawo kan lamarin yayin da aka mika wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Tashar wutar lantarkin ita ce dai babbar kafar hannun jari na fiye da dala biliyan 2 daga ketare ga kasar ta Bangladesh, kuma guda daga cikin ayyukan China na kokarin kara kusanci da Dhaka